Gobara ta farko ta tashi ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, a wata tashar wutar lantarki da ke Dan Agundi. Hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa da misalin 茩arfe 9:52 na safe, inda jami鈥檃nta suka isa wurin suka tarar da wani fili mai girman kusan 茩afa 200 da 100 cikin wuta. Gobarar ta shafi transfoma 蓷aya, amma jami鈥檃n kashe gobarar sun yi nasarar shawo kanta kafin ta bazu zuwa wasu sassan wurin.
Gobara ta biyu kuma ta tashi a ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026, a kamfanin NUTAK Universal Company Limited, da ke Kwakwaci kusa da Bola a 茦aramar Hukumar Fagge. An samu kiran gaggawa da misalin 茩arfe 9:05 na safe, inda jami鈥檃n tashoshin kashe gobara na Central da Bompai suka isa wurin.
A wurin, jami鈥檃n sun tarar da ginin bene na 茩asa mai girman kusan 茩afa 50 da 100 cikin wuta. Gobarar ta shafi bandaki, gangunan sinadarai 25, kwalaben fenti guda 600 masu girman lita hu蓷u, injinan samar da kaya 10 da kuma wuraren ajiyar fenti guda uku na 茩ar茩ashin 茩asa, wa蓷anda gobarar ta mamaye gaba 蓷aya. Wani 蓷akin ajiya kuma ya 蓷an samu matsala.

1
Hukumar ta ce mutane biyu sun samu matsala sakamakon gobarar kafin isowar jami鈥檃n kashe gobara, amma an samu nasarar ceto su da ransu. Jami鈥檃n kashe gobara sun yi amfani da kayan aiki wajen shawo kan gobarar tare da hana ta 茩ara ya蓷uwa.
A cewar jami鈥檌n hul蓷a da jama鈥檃 na Hukumar Kashe Gobara ta Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, har yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar guda biyu.
Hukumar ta kuma yi kira ga jama鈥檃 da su kasance cikin taka-tsantsan, tare da gaggauta sanar da jami鈥檃n kashe gobara idan gobara ko wata matsalar gaggawa ta taso. Ta kuma shawarci kamfanoni da wuraren da ake amfani ko adana abubuwa masu saurin kama wuta da su kiyaye matakan kare gobara.





