Tsagaita wutar ta shafi garin Oleshky da yankunan da ke kewaye da shi, inda aka amince da dakatar da faɗa na tsawon kwanaki shida domin bai wa fararen hula damar fita daga wuraren da rikicin ya fi kamari.
Rahoton ya bayyana cewa an yi nasarar kwashe fararen hula 167 daga wasu yankuna masu haɗari a kudancin Kherson a ranar Lahadi, bayan ƙarewar wa’adin tsagaita wutar. Daga cikin mutanen akwai yara da kuma wasu masu buƙatar taimako na musamman.
An cimma wannan matsaya ne bayan ƙoƙarin shiga tsakani da uwargidan shugaban Amurka, Melania Trump, ta taka rawa a ciki, tare da sa hannun Paparoma Leo. An ce babu wani ɓangare da ya bayar da rahoton keta yarjejeniyar a lokacin da take aiki.
A wani ɓangaren kuma, rundunar sojin Ukraine ta ce ana zargin an yi kutse cikin manhajar wayar da ake amfani da ita wajen aika gargaɗin hare-haren sama. Manhajar ta nuna saƙonnin ƙarya na barazanar makaman nukiliya da sinadarai a Kyiv da wasu yankuna, lamarin da ya sa rundunar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu.
Ƙarewar wannan tsagaita wuta na zuwa ne yayin da rikicin Rasha da Ukraine ke ci gaba, duk da ƙoƙarin neman mafita ta diflomasiyya. Rahoton ya kuma nuna cewa ana sa ran tattaunawar sulhu da Amurka ke shiga tsakani za ta sake gudana a wannan watan, bayan dakatar da ita na wani lokaci.





