Tinubu ya ce cire tallafin man fetur, gyaran tsarin musayar ku蓷a蓷en waje, 茩ara tattara ku蓷a蓷en shiga da zuba jari a manyan ababen more rayuwa sun fara kawo sauyi a tattalin arzikin 茩asar. Shugaban, wanda Shugaban Jam鈥檌yyar APC na 茦asa, Nentawe Yilwatda, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a wani taron baje kolin ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a Abuja.

1
Ya ce ajiyar ku蓷a蓷en waje na Najeriya ta kai kusan dala biliyan 52.7, yayin da GDP ya 茩aru da kashi 4.43 cikin 蓷ari a zangon farko na shekarar 2026, sannan hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kusan kashi 15.4 cikin 蓷ari.
Sai dai Shugaba Tinubu ya amince cewa har yanzu akwai 茩alubale, yana mai cewa ainihin nasarar sauye-sauyen za ta bayyana ne idan sun haifar da raguwar farashin abinci, 茩arin guraben ayyukan yi, samun rance cikin sau茩i da ingantaccen samar da wutar lantarki ga 鈥檡an Najeriya.




