Fadar ta bayyana hakan ne yayin da ta kar蓳i ba茩uncin Mataimakin Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Mista Pedro Sarayo, wanda ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Kano a fadarsa.
A yayin ziyarar, an tattauna kan muhimmancin ha蓷in gwiwa tsakanin hukumomi da kungiyoyin 茩asa da 茩asa wajen inganta rayuwar al鈥檜mma, musamman a fannoni irin su lafiya, ilimi, noma, al鈥檃du da fasahar zamani.

glob hub
Da yake jawabi a madadin Fadar Masarautar Kano, Babban 茒an Majalisar Masarautar Kano kuma Matawallen Kano, Alhaji Aliyu Ibrahim Matawalle, ya bayyana cewa Fadar Kano na da masaniya kan ayyukan da Tarayyar Turai ke gudanarwa a Najeriya.
Ya ce irin wa蓷annan shirye-shirye na taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa al鈥檜mma da kuma bun茩asa fannoni daban-daban da suka shafi rayuwar 鈥檡an 茩asa.
Alhaji Aliyu Ibrahim Matawalle ya bayyana cewa ayyukan da EU ke tallafawa sun ha蓷a da shirye-shirye a fannonin lafiya, ilimi, noma da sauran ayyukan da ake aiwatarwa domin inganta jin da蓷in al鈥檜mma.
Ya 茩ara da cewa Masarautar Kano tana maraba da duk wani shiri da zai taimaka wajen kawo ci gaba da inganta rayuwar al鈥檜mmar Kano da Najeriya baki 蓷aya.
A cewarsa, Majalisar Masarautar Kano a shirye take ta ba da ha蓷in kai da goyon baya ga shirye-shiryen da aka tsara domin amfanin al鈥檜mma, musamman wa蓷anda za su taimaka wajen inganta rayuwa da samar da damammaki ga matasa da sauran 蓳angarorin al鈥檜mma.
Ya kuma yi wa tawagar Tarayyar Turai fatan samun kyakkyawar zama a Najeriya da kuma gudanar da ayyukansu cikin nasara.
Tun da farko, shugaban tawagar Tarayyar Turai, Mataimakin Jakadan EU a Najeriya, Mista Pedro Sarayo, ya bayyana cewa ziyarar tasu ta kasance ne domin nuna girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Kano da kuma 茩arfafa dangantakar dake tsakanin Tarayyar Turai da Najeriya.
Mista Sarayo ya ce Tarayyar Turai na da aniyar ci gaba da tallafawa Najeriya a fannoni daban-daban na ci gaban jin 茩ai da bun茩asa rayuwar al鈥檜mma.
Ya bayyana cewa baya ga fannoni da EU ta dade tana tallafawa, 茩ungiyar tana kuma duba wasu sabbin hanyoyi na ha蓷in gwiwa da suka shafi al鈥檃du, fasahar zamani da harkokin dijital.
A cewarsa, sabbin dabaru da shirye-shiryen na da nufin 茩arfafa damar al鈥檜mma da kuma samar da hanyoyin da za su taimaka wajen ci gaban Najeriya.




