Sakamakon Ćuriâun da aka Ćirga ya nuna cewa Yotova ta samu kusan kashi 57.58 cikin 100 na Ćuriâun da aka kaÉa, inda ta doke abokin hamayyarta, Andrey Gyurov, wanda ya samu kashi 39.46 cikin 100.
Wannan nasara ta sa Yotova ta zama mace ta farko da aka zaÉa kai tsaye domin shugabantar Ćasar Bulgaria. Ta kuma samu gagarumar nasara a gundumomi da dama na Ćasar, yayin da Gyurov ya amince da sakamakon zaÉen tare da taya ta murna.
A zagayen farko na zaÉen da aka gudanar a makon da ya gabata, Yotova ta samu kashi 34.76 cikin 100 na Ćuriâu, yayin da Gyurov ya samu kashi 31.95. Rashin samun rinjayen da ake buĆata ne ya sa aka gudanar da zagaye na biyu tsakanin âyan takarar biyu.
A lokacin yaĆin neman zaÉe, Yotova ta bayyana matsayarta na adawa da Ćarin tallafin makamai ga Ukraine, inda ta fi karkata ga neman hanyar diflomasiyya domin kawo Ćarshen yaĆin da Rasha. Wannan matsaya ta bambanta da ta abokin hamayyarta, wanda ya fi nuna goyon baya ga Ćarfafa haÉin gwiwar tsaro da Ćasashen Yamma.
Nasara ce mai muhimmanci ga Yotova, wadda ta taÉa riĆe muĆamin mataimakiyar shugaban Ćasa kafin ta zama shugabar riĆon Ćwarya a watan Janairun bana. Ana sa ran za ta jagoranci Ćasar na waâadin shekaru biyar, yayin da ake sa ido kan yadda za ta tafiyar da alaĆar Bulgaria da Tarayyar Turai da kuma batun yaĆin Ukraine.





