Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Fadar Masarautar Dutse a Jihar Jigawa, inda ya kuma kai taâaziyya bisa rasuwar Mai Martaba Sarkin Gumel. Sarkin ya je ziyarar ne tare da wasu daga cikin manyan hakimansa na Masarautar Kano.
Khalifa Muhammadu Sanusi na II ya bayyana jin daÉinsa da yana mai cewa âwannan ziyara ta kasance wata dama ta sada zumunci da Ćarfafa alaĆa tsakanin Masarautun Kano da Dutse.â

2
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamid Sanusi, ya bayyana ziyarar Sarkin Kano a matsayin mai matuĆar muhimmanci, inda ya ce âwannan ziyara za ta Ćara Ćarfafa alaĆar da ke tsakanin masarautun biyuâ
Ya kuma yi fatan alheri ga Masarautar Kano da alâummar Jihar Kano, tare da jaddada buĆatar ci gaba da Ćarfafa zumunci da haÉin kai tsakanin masarautun.




