Sarkin ya fito ne ta Kofar Kwaru, ya bi ta titin Mandawari zuwa Kwanar Diso, sannan ya bulla ta Galadanci zuwa Gwale, yayin da dubban al鈥檜mma suka yi cincirindo a gefen hanyoyin domin kallon hawan da yi wa Mai Martaba gaisuwa.
Abin da ya fi jan hankali yayin hawan shi ne yadda Mai Martaba ya ri茩a tsayawa a duk lokacin da ya ga taron jama鈥檃, domin yi musu addu鈥檕鈥檌n neman zaman lafiya, ha蓷in kai da kwanciyar hankali a tsakanin al鈥檜mmar Kano.

1
Daga cikin mutanen da Sarkin ya tsaya a wurinsu akwai tsohon Al茩ali, Bashir Ahmad, wanda ya gabatar da gaisuwar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Kano.
A halin yanzu, Mai Martaba yana kusa da Asibitin Yara na Hasiya Bayero, inda yake kar蓳ar gaisuwa daga hakimai da al鈥檜mma daban-daban da suka fito domin nuna masa goyon baya da girmamawa.

1
Daga bisani Mai Martaba ya sauka daga kan dokinsa, inda ya hau rakumi domin ci gaba da hawan zuwa sauran wuraren da aka tanada, yayin da jama鈥檃 ke ci gaba da tururuwa domin ganin wannan gagarumin biki na Hawan Maulidi.




