Kamfanin ya ce zai dauki matakin shari’a kan duk wani mutum ko kafar yada labarai da za ta ci gaba da yada bayanan karya da ke iya bata masa suna ko haifar da rudani tsakanin kwastomominsa.
OPay ta bukaci jama’a da su dogara da sahihan bayanai daga hanyoyin sadarwarta na hukuma, tare da yin watsi da duk wani sako da ba a tabbatar da sahihancinsa ba.





