Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya bayyana cewa maharan sun kai hare-hare kan wasu muhimman wurare, amma jami鈥檃n tsaro sun yi gaggawar mayar da martani, lamarin da ya taimaka wajen dakile harin tare da kwato iko da wuraren da lamarin ya shafa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Janar Modi ya ce al鈥檃mura sun fara komawa daidai, yayin da jami鈥檃n tsaro ke ci gaba da tabbatar da tsaron muhimman wurare a birnin Niamey.
Ya kuma ce al鈥檜mmar birnin na cikin kwanciyar hankali, kuma suna ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin 鈥檡anci, ba tare da wata matsala ba.
Wannan sabon hari ya zo ne bayan makamancin wani hari da Nijar ta fuskanta a watan Janairun 2026, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji, kafin jami鈥檃n tsaron kasar su dakile harin tare da kashe wasu daga cikin maharan.




