Tasnim, wadda ke da alaƙa da Rundu
nar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, ta ruwaito cewa sansanonin Amurka sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da mirage marasa matuƙa na Iran.

1
Sai dai har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, Tasnim ba ta bayar da cikakken bayani kan irin barnar da aka samu ko kuma adadin waɗanda abin ya shafa ba. Haka kuma, ba a samu martani daga hukumomin sojin Amurka kan wannan ikirari ba.
Tsauraran matakan takaita yaɗa bayanai da ake gani a wasu ƙasashen yankin Tekun Fasha na sanya samun bayanai kai tsaye daga wuraren da ake kai hare-hare cikin wahala. Haka kuma, ana ƙara sa ido kan hotunan tauraron ɗan adam da ke nuna wuraren soji.
A ranar Laraba, Tasnim ta kuma wallafa wasu hotunan sama da ta danganta da hare-haren Iran kan sansanonin Amurka a Jordan, tana mai cewa hotunan sun nuna barnar da hare-haren suka haddasa.




