Gobara ta farko ta tashi ne da misalin ƙarfe 1:17 na rana a reshen bankin Access Bank da ke Dawanau, Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, bayan hukumar ta karɓi kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin mai suna Michael.

1
Jami’an hukumar kashe gobara na tashar Dawanau sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka tarar da gobarar ta kama janaretan Mikano da kuma wani na’urar canza wutar lantarki. Sai dai jami’an kashe gobarar sun samu nasarar shawo kan lamarin tare da hana wutar yaɗuwa zuwa sauran sassan ginin bankin. Har yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar.
A wani lamari makamancin haka, gobara ta biyu ta tashi da misalin ƙarfe 6:19 na yamma a yankin Sabuwar Gandu, Sheka Gari, Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

2
Jami’an kashe gobara daga tashar Sharada Industrial Area sun isa wurin, inda suka tarar da gobarar ta kama ɗakuna biyu, falo da kuma ɗakin girki na wani gidan zama.
Jami’an sun yi nasarar shawo kan gobarar ta hanyar amfani da bututun ruwa guda ɗaya daga motar kashe gobara ta Commando 3, Sharada, tare da ƙarin bututun ruwa guda biyu daga wasu masana'antu da ke kusa.
Hukumar ta ce har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba, kuma ana ci gaba da bincike.
Daraktan Hukumar, Alhaji Sani Anas, ya yi kira ga jama’a da su ƙara taka-tsantsan tare da ɗaukar matakan kariya domin rage yawaitar gobara.
Ya kuma shawarci mazauna jihar da su samar da na’urorin kashe gobara masu aiki a gidajensu, tare da bin ƙa’idojin kiyaye gobara a kowane lokaci.




