An bai wa Darakta Janar na Hukumar Kula da Alhazai ta Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, lambar yabon ne saboda jajircewa da ĆoĆarinsa wajen tallafa wa ayyukan Hukumar Shige da Fice, musamman wajen tabbatar da cewa mahajjatan Kano sun samu fasfo cikin sauĆi ba tare da jinkiri ba.
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Alhazai ta Kano, Suleman Dederi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Yayin bikin miĆa lambar yabon, Jamiâin Kula da Fasfo na Farm Centre, Kano, Alhaji Aliyu Hamisu Nguroje, ya yaba wa Matawalle bisa kulawar da yake bai wa mahajjatan jihar.

2
Ya ce a lokacin aikin Hajjin da ya gabata, Daraktan ya nuna Ćwazo wajen tabbatar da cewa mahajjatan sun samu dukkan taimakon da suke buĆata yayin neman fasfo.
A nasa jawabin, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle ya gode wa Hukumar Shige da Fice bisa karramawar, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da Ćarfafa haÉin gwiwa da hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki domin sauĆaĆa wa alâummar Kano gudanar da aikin Hajji.
Ya kuma yaba wa Ofishin Fasfo na Farm Centre bisa haÉin gwiwa da kuma ĆoĆarin da yake yi wajen hanzarta fitar da fasfo ga mahajjata, tare da tabbatar da cewa ba a samu jinkirin da ba dole ba.




