Dangote ya bayyana hakan ne a Kano a yau Alhamis, yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce hankalinsa a yanzu ya fi karkata wajen gudanar da kamfanoninsa da sauran manyan ayyukan kasuwancinsa.

Chat Gpt
Da yake karin bayani kan batun yayin wata hira da wakilin Premier Radio, Abubakar Haruna Galadanchi, Dangote ya ce a baya ya yi kokarin tattaunawa da masu kungiyar Arsenal kan yiwuwar mallakar wani kaso ko kuma sayen kungiyar.
Sai dai ya bayyana cewa yanzu ba ya shirin ci gaba da wannan yunkuri, ko da yake zai ci gaba da kasancewa mai goyon bayan Arsenal, tare da kallon wasannin kungiyar idan ta buga a birnin London.
A baya, Aliko Dangote ya sha bayyana sha鈥檃warsa ta mallakar Arsenal, kungiyar da ya dade yana nuna goyon bayanta.
Sai dai Dangote ya ce a halin yanzu hankalinsa ya karkata ne ga kamfanonin da yake jagoranta, wadanda yake ganin suna bukatar kulawarsa sosai yayin da yake kokarin fadada harkokin kasuwancinsa.
Dangote Group a halin yanzu na gudanar da manyan ayyuka da suka hada da matatar Dangote, wadda ta fara sayar da hannun jari ga jama鈥檃 ta hanyar IPO a wannan watan, a wani shiri da ke neman kara fadada mallakar kamfanin ga masu zuba jari.





