KANO: ’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Zargin Kisan Dan Shagamu
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan fitaccen mai sharhi a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Dan Shagamu. An kashe marigayin ne a gidansa da ke Gaida Quarters, Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano.
Sep 11, 2026 · 1 min read












