Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da Premier Radio a Dutse, inda ya ce an cafke wanda ake zargin ne bayan jami’an tsaro sun tare wasu ’yan kasuwa a kan hanyarsu ta komawa gida daga Kasuwar Machina da ke Jihar Yobe, zuwa Birniwa a Jihar Jigawa.
A cewar SP Lawan Shiisu Adam, rundunar ta samu nasarar cafke wanda ake zargin shugaban ƙungiyar ne bayan gudanar da samamen tsaro da kuma bin diddigin bayanan da suka samu dangane da ayyukan ƙungiyar.
Ya ce ana zargin ƙungiyar da aikata laifukan fashi da makami da kuma addabar matafiya a wasu hanyoyin da suka haɗa yankunan Hadejia, Malam Madori da Birniwa. Rundunar ta ce bincike kan wanda ake zargin da sauran waɗanda ake dangantawa da ƙungiyar na ci gaba.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da sintiri da samame domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen dakile ayyukan masu aikata laifuka.





