Obi ya bayyana hakan ne a wajen Taron Tattaunawar Dimokuraɗiyya na Goodluck Jonathan Foundation na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Bauchi. Ya ce abin takaici ne yadda wasu masu ilimi da ya kamata su kasance masu kare dimokuraɗiyya ke shiga harkokin da ka iya lalata tsarin zaɓe.
Ya kuma soki yadda ake gudanar da wasu ayyukan zaɓe, musamman yadda ake samun takaddama kan sakamakon zaɓe da zargin sauya sakamako, tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a da sauran hanyoyin da ka iya gurgunta sahihancin zaɓe.
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya kuma zargi wasu alkalai da nuna son kai, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun zama masu biyayya ga jam’iyyar da ke mulki. Ya kuma soki Majalisar Dokoki ta Ƙasa kan cire laifin jabun takardu daga cikin wasu laifukan da suka shafi zaɓe.
Peter Obi ya ce waɗannan abubuwa na nuni da babbar matsalar hukumomi a Najeriya, yana mai kira da a gaggauta yin gyare-gyaren da za su dawo da amincewar jama’a tare da ƙarfafa dimokuraɗiyya da sahihancin zaɓe a ƙasar.

1





