Matakin ya biyo bayan umarnin shugabancin Majalisar da ya bukaci kwamitocin da su kammala ayyukansu tare da gabatar da rahotannin da suka rage. A cewar sanarwar da Magatakardan Majalisar, Sidi Ibrahim, ya sanya wa hannu, kwamitocin wucin gadi guda biyu ne kawai suka nemi 茩arin lokaci, kuma wa'adin makonni biyu da aka ba su ya 茩are.
Majalisar ta bayyana cewa kwamitocin wucin gadi ana kafa su ne domin gudanar da ayyuka na musamman da aka kayyade musu lokaci, don haka ba za su ci gaba da aiki bayan wa鈥檃din da aka ba su ba. An umarci shugabannin kwamitocin da su mi茩a dukkan rahotanni, takardu da sauran bayanan da suka shafi ayyukansu ga Ofishin Magatakardan Majalisar domin adanawa.





