Kwankwaso ya bayyana Adeleke a matsayin abokinsa, yana mai cewa nasarar ta nuna yadda al’umma ke da ikon bayyana ra’ayinsu ta hanyar zaɓe. Ya kuma yaba wa al’ummar Osun bisa yadda suka fito suka sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu na zaɓar shugabanninsu.

1
A cikin saƙon nasa, Kwankwaso ya kuma yaba wa INEC kan yadda ta gudanar da zaɓen, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tabbatar da cewa zaɓuka a Najeriya suna gudana cikin gaskiya, zaman lafiya da kuma gaskiya.





