An gudanar da taron tabbatar da takararsa, wanda ya samu halartar dandazon al’umma da magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya, waɗanda suka fito domin nuna goyon bayansu ga takarar Garo.

1
Taron ya kasance wani muhimmin mataki na shirye-shiryen jam’iyyar NDC da magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya gabanin zaɓen 2027, yayin da Garo zai nemi wakiltar mazabar Sanatan Kano ta Arewa a Majalisar Dattawa.





