Bill Gates ya bayyana hakan ne a cikin wata doguwar makala mai kalmomi kusan 6,000, mai taken “The turbulent AI era is here. The choices we make now are critical.” Ya ce AI na iya zama babbar fasahar da za ta taimaka wajen daidaita damammaki tsakanin mutane, amma kuma tana iya zama sanadin rashin adalci mafi muni idan aka yi amfani da ita ba tare da tsari ba.
A cewarsa, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ci gaban AI bai jefa al’umma cikin matsaloli ba.
Gargadin Gates na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yadda wasu nau’ikan AI ke aiki da kuma yiwuwar fasahar ta rage guraben ayyukan yi, musamman ga wasu ma’aikata. Duk da haka, kamfanonin fasaha da masu zuba jari a kasuwannin duniya na ci gaba da ƙara saka hannun jari wajen haɓaka wannan fasaha.
Gates ya jaddada cewa makomar AI za ta dogara ne da matakan da duniya za ta ɗauka a yanzu, yana mai cewa ya kamata a tabbatar da cewa fasahar ta kasance mai amfani ga kowa, ba wai ta ƙara haifar da rashin daidaito da cutarwa ga bil’adama ba.




