Marigayin ya shafe sama da shekaru 45 yana kan karagar mulkin Masarautar Gumel, bayan hawansa karagar mulki a shekarar 1981. Rasuwarsa ta jefa al鈥檜mmar Masarautar Gumel da Jihar Jigawa cikin jimami.
An haifi Sarkin Gumel a ranar 12 ga Disamba, 1942, kuma kafin hawansa karagar mulki ya yi aiki a fannoni daban-daban na gwamnati, ciki har da zama Kwamishinan Ya蓷a Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al鈥檃du na tsohuwar Jihar Kano.
Rasuwar Mai Martaba na zuwa ne 茩asa da shekara guda bayan gudanar da bikin cika shekaru 45 da hawansa karagar mulki, abin da ya sa rasuwar ta zama babban rashi ga Masarautar Gumel da al鈥檜mmar jihar Jigawa.
A halin yanzu, ana jiran 茩arin bayani daga Masarautar Gumel da gwamnatin Jihar Jigawa kan shirye-shiryen jana鈥檌zar marigayin da lokacin da za a gudanar da sallar jana鈥檌zarsa.




