A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, Adeleke ya danganta nasarar da ya samu da ikon Allah da kuma goyon bayan al’ummar Jihar Osun, yana mai cewa jam’iyyar ADC ba ta cikin ƙungiyar haɗin gwiwar siyasa ta “Rainbow Coalition” da ta yi kamfe, tattara jama’a da kuma tallafa wa yaƙin neman zaɓensa.

1
Gwamnan ya kuma yaba wa abokan siyasarsa da magoya bayansa bisa irin gudunmawa, sadaukarwa da ƙoƙarin da suka bayar wajen ganin ya samu nasarar lashe zaɓen tare da komawa wa’adi na biyu.





