Da yake magana kan wannan nasara, Idris ya ce akwai buƙatar samar da hanyoyin da za su sauƙaƙa wa ’yan kasuwar Najeriya shiga kasuwannin ƙasashen waje. Ya ce hakan zai taimaka wa kamfanonin Najeriya wajen samun sababbin kwastomomi, jawo jarin ƙasashen waje da kuma samar da guraben ayyukan yi ga matasa.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su samar da ingantattun manufofi da yanayin kasuwanci mai kyau, domin ƙarfafa ’yan kasuwa su faɗaɗa harkokinsu zuwa ƙasashen duniya. Idris ya ce bunƙasar kamfanonin Najeriya a ƙasashen waje ba za ta amfanar da masu kamfanonin kaɗai ba, har ma za ta taimaka wajen samar da ayyukan yi da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.


